Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Labarin ya kara da cewa, wannan shi ne satar mutane ta baya-bayan nan wanda aka yi a jihar, a cikin jerin sace-sacen mutane wanda ya zama ruwan dare a kasar. Labarin ya kara da cewa mafi yawan sace-sacen na neman kudaden fansa ne daga dangi da abokan wadanda aka sacen.
Wani wanda ya ganewa idanunsa mai suna Habu Abubakar dan garin Rini kauyen da aka yi satar, ya ce yawan mutanen da ‘yan bindigan suka tafi da su ya kai 80. Abubakar ya ce ‘yan bindigan wadanda yawansu ya fi 50 sun shigo kauyen Rini ne, haye a kan Babura.
Abubakar ya fadawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa sun yashe shagonsa, ba abinda su ka rage masa sai kayaki kadan. Kakakin ‘yansa a jihar Zamfara ya tabbatar da labarin.
342/